Hukumar shari’a a Kano ta yi wa wani ma’aikacin ta ritayar dole bisa zargin karbar cin hanci

-

Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta jihar Kano (JSC), ta dakatar da wani jami’in ta tare da yi wa wani ritayar dole saboda karbar cin hanci.

Kakakin hukumar, Baba Jibo, shi ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa hukumar ta amice da hukuncin da aka dauka kan ma’aikatan a taronta na 79 da ta gudanar a ranar 6 ga watan Fabrairu wanda babban alkalin jihar, Dije Aboki ta jagoranta.

Ya ce binciken da kwamitin sauraron korafe-korafen jama’a na sashen shari’a (JPCC) ya yi dangane da karar da wani Alhaji Sani Bozo Rimin Gado ya shigar a kan Hudu Idris wato magatakarda a kotun shari’a ta Upper Shari’a Gwarzo da Abba Bala Gwarzo, mai gadi a kotun.

Ana zargin  jami’an kotunan biyu da yi musu barazana da kuma neman kudi ba bisa ka’ida ba. 

Bayan wani kwakkwaran bincike, mutanen biyu sun bayyana a gaban hukumar ta JPCC, inda suka amsa laifin cewa suna da hannu a cikin almundahana da ya kai na N214,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara