DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu a Abuja ta dakatar da Majalisar Dattawa daga ladabtar da Sanata Natasha

-

 

Sanata Natasha Akpoti

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da kwamitin da’a na majalisar dattawa da karbar koken jama’a daga ladabtar da sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan.

Google search engine

Alkalin kotun, Obiora Egwuatu, ya ba da umarnin ne a ranar Talata bayan wata takardar karar da lauyan Akpoti-Uduaghan ya shigar a gaban kotun.

A ranar 20 ga watan Fabrairun shekarar 2025, sanatar mai wakiltar Kogi ta tsakiya ta yi musayar kalamai da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kan batun sauyin wurin zama da aka yi mata.

Kin bin umarnin shugaban majalisar Godswill Akpabio da ta yi, ya janyo cece kuce a cikin majalisar da ma wajen majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tankiya tsakanin Nijer da Benin ta sa kasashen rufe ofisoshin jakadancin juna

Kasashen Benin da Niger sun kori jami’an diflomasiyyar juna a wani mataki na ramuwar gayya, bayan shafe kusan shekara biyu ana takun-saka a tsakaninsu, a...

‘Yan bindiga sun yi ajalin mutane fiye da 30 a jihar Neja

Aƙalla mutane 30, ciki har da mata, sun rasu bayan da ‘yan bindiga suka kai hari Kasuwan Daji da ke ƙauyen Demo, Borgu LGA a...

Mafi Shahara