DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gidauniyar Dangote ta samar da abinci na Naira bilyan 16 ga talakawan Nijeriya

-

Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, wanda aka kaddamar a ranar Alhamis, ta ware kudi kimanin Biliyan16 domin tallafa wa ralakawa ‘yan Najeriya masu nakasa da kuma marasa karfi.
Sama da mutum miliyan daya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan shinkafa mai nauyin kilo gram 10 daga wannan tsarin na gidauniyar Aliko Dangote.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar, shugaban gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an tsara yin rabon shinkafar buhu miliyan daya ne mai nauyin kilo gram 10, ga ‘yan Najeriya marasa karfi da raunana, a kananan hukumomi 774 na kasar, kamar yadda yake a tsarin kamfani da kuma gidauniyarsa na nuna jinkai ga ‘yan kasar.
Dangote, wanda ya samu wakilcin diyarsa, Hajiya Mariya Aliko Dangote, ya ce: shirin na wannan shekara, an yi shi ne da nufin nuna tausayi da jinkai da nuna kulawa wajen taimakon jama’a bisa la’akari da halin da ake ciki na matsin rayuwa da durkushewar tattalin arziki.
Ya ce gidauniyar ta fara kaddamar da rabon tallafin ne a jihar Kano, bayan nan za a ci gaba da rabawa zuwa sauran jihohi, domin tabbatar da ganin cewa abincin ya isa hannun wadanda aka yi domin su a daukacin kananan hukumomin Nijeriya.
Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar Alhaji Aliko Dangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a daukacin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano.
A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko Dangote, Zouera Youssoufou ta ce an tsara shirin ne a matsayin wata hanya ta tallafa wa gwamnatoci wajen yaki da talauci da yunwa a Nijeriya.
Mukaddashin Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Dr. Mujahid Aminudden ya gode wa gidauniyar ta Dangote kan bijiro da wannan shiri, inda ya roki sauran ‘yan Nijeriya da suyi koyi da halin Dangote.
Ya ce Hukumar Hisbah za ta tsaya tsayin daka wajen ganin tallafin yaje hannun wadanda suka cancanta.
Wani da ya yi magana a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin mai suna Ibrahim Ahmed ya yaba wa Aliko Dangote, inda ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da taimakonsa a harkokinsa na kasuwanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsohon Minista Tanimu Turaki ya zama ɗan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na Arewa

Jagororin jam’iyyar PDP na yankin Arewacin Nijeriya sun amince da tsohon Ministan Harkoki. A Musamman, Tanimu Turaki (SAN), a matsayin ɗan takarar da suka amince...

Jam’iyyar ADC a Kaduna ta kori mataimakin shugabanta da wasu ‘ya’yanta 8

Jam'iyyar hadaka ta ADC mai hamayya a Nijeriya reshen Kaduna ta kori mataimakin shugabanta na jihar tare da wasu manyan jami'anta guda takwas, bayan samun...

Mafi Shahara