![]() |
Bala Abdulkadir Muhammad |
Gwamnatin jihar Bauchi ta ce kama Akanta Janar na jihar da aka yi, Alhaji Sirajo Mohammed, inda ta bita da kullin siyasa ne.
A cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Alhaji Mukhtar Gidado ya fitar, gwamnatin ta ce yadda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ke gudanar da ayyukanta na tayar da hankali matuka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa abin mamakine yadda aka kama Akanta Janar din domin,idan har an gayyacesa domin neman wasu bayanai zai je,amma hakan na nuni da cewa akwai wani bita da kullin siyasa a ciki domin hakan ya sanya shakku ga al’umma