![]() |
Abdulrahmanee Tiani |
Bikin nada Janar Tiani a matsayin janar na hafsoshin sojin Nijar ya cimma matsayar cewa daga wannan rana, Janar din ya yi wa fursunonin siyasa afuwa amma ban da Bazoum Mohammed sannan gwamnatin mulkin sojin ta Nijar ta soke jam‘iyyun siyasa gaba daya har sai an ga abin da hali ya yi.
Rahoton da DCL Hausa ta samu kuma ya nuna cewa sojojin sun amince da su yi shekaru biyar suna jagorantar gwamnatin rikon kwarya, idan tsaron kasa ya bayar da dama za a iya komawa siyasa amma idan babu dama gwamnatin za ta iya ci gaba da wanzuwa bayan shekaru biyar.