Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya ba da umarnin gudanar da bincike bisa ajalin wasu mafarauta da aka yi da ya tayar da hankulan jama’a a yankin Uromi ta jihar
Wasu da ake zargin ’yan daba ne dai sun kama wadanda aka halaka a Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a Jihar Edo,bayan sun tafi da motarsu inda aka gano bindigogin da mafarauta ke amfani da su, ’yan garin sukai zargin masu garkuwa da mutane ne, inda suka kona su da ransu.
A cikin wani faifan bidiyo da angano wasu matasa na cinnawa mutanen wuta da ransu a yankin na Uromi a jihar ta Edo.