DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan sandan Kano sun haramta hawan Sallah

-

 

Google search engine

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta hawan Sallah da bukukuwan karamar Sallah na 2025, saboda dalilan tsaro da kuma bukatar tabbatar da zaman lafiya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya sanar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan Bompai, ranar Juma’a.

CP Bakori wanda ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin bukukuwan Sallar ya ce bisa bincike da aka yi a fannin tsaro, ya nuna karuwar tashe-tashen hankula da kuma barazanar da ke tattare da hawan Sallah wanda zai iya haifar da tarzoma.

Ya ce biyo bayan rahotannin sirri da hukumar ta samu na tsare-tsaren wasu miyagu da aka dauki nauyinsu na yin amfani da bikin Sallah wajen kawo tarzoma, rundunar ‘yan sandan tare da tuntubar gwamnatin jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, ta yanke shawarar haramta duk wani biki a lokacin bikin sallar.

Kwamishinan ya tabbatar wa mazauna garin cewa an samar da isassun matakan tsaro don kare al’umma yayin Sallar Idi a wuraren da aka kebe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tinubu ya gargadi Alkalan Nijeriya da kada su karkata ga cin hanci ko rashin adalci

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga alkalai da sauran ma’aikatan shari’a a Najeriya da su ci gaba da zama masu gaskiya, adalci,...

PDP ta musanta zargin kirƙirar sa hannun Sakataren ta na kasa

Kwamitin zartaswa na Ƙasa na jam’iyyar PDP ya musanta zargin ƙirƙirar sa hannu da Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya yi. Mai magana da...

Mafi Shahara