![]() |
Janar Maharazu Tsiga |
Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana damuwarta kan yadda ake yada labarai cewa wasu manyan hafsoshin soja sun tara kudi domin ceto tsohon Birgediya Janar Mahrazu Tsiga (rtd), wanda ya shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa.
A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ya ce wannan ikirari na wani tsohon hafsan soja, Ismaila Abdullahi, na iya rage kimar aikin da rundunar Operation Fanjan Yamma ta gudanar domin ceto Janar Tsiga.
A cewar Gusau, sojojin Najeriya sun aiwatar da dogon bincike da kai samame da hare-haren sama, lamarin da ya tilasta masu garkuwan tserewa suka bar Janar Tsiga.
Ya ce irin wadannan maganganu na iya kawo tangarda ga kwazon dakarun kasa, tare da bude kofar suka daga bangarori masu adawa da sojoji, duk da cewa bai musanta cewa an tara kudaden ba.