Wata kwararriyar mai bincike kan harkokin da suka shafi mata Ololade Alayi ta koka kan yadda ake samun karuwar ajalin mata a Nijeriya, inda bincikenta ya gano cewa tsakanin watannin Janairu da Fabrairun 2025 kadai, an yi ajalin mata 34, a watan Maris kuwa aka samu 16 a Nijeriya.
Ms. Ololade ta bayyana cewa, duk da cewa adadin da aka ambata ya shafi watan Janairu da Fabrairu, DOHS Foundation ta riga ta samu rahoton ajalin mata guda uku a watan Maris, wadanda suka faru kafin ko a ranar 8 ga Maris, ranar da aka gudanar da bikin makon mata na Duniya.
Ta kara da cewa, a watan Janairu an yi ajalin mata guda 17, yayin da a watan Fabrairu aka samu guda 15, Kuma adadin na ci gaba da karuwa, a cewar Ololade, wannan karuwar mummunan lamari kan mata na nuna cewa a duk kwana biyu, ana ajalin mace guda a Najeriya.
A cikin rahoton Hukumar Amnesty International, na shekarar 2024, mata da ‘yan mata guda 149 ne aka yi ajalisu Najeriya. A matakin duniya kuwa, rahoton Hukumar Mata ta Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2024 ya bayyana cewa a shekarar 2023, mata da ‘yan mata guda 85,000 aka kawar, wanda kasha 60% na wadannan abin ya shafa an yi su ne da hannun abokan zama ko ‘yan uwa.