DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kwankwaso ba zai koma jam’iyyar APC ba – Buba Galadima

-

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi watsi da ikirarin da ake na cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar APC.

Ya ce jam’iyyar NNPP ta bai wa ‘yan Nijeriya damar fahimtar abubuwan da jam’iyyar za ta iya yi ta hanyar ingantaccen shugabanci mai cike da gaskiya da rikon amana.

Google search engine

Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr,Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen komawar Kwankwaso jam’iyyar APC, inda ya jaddada cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na shirin yin shiga.

Ganduje, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar magoya bayan Tinubu, wadanda suka kai masa ziyara a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na ci gaba da karbar fitattun ‘yan siyasa ciki har da ‘yan majalisar tarayya.

Ya kara da cewa jam’iyyar na dakon dawowar Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Real Madrid na da shiga rai amma burina yin nasara tare da Arsenal – William Saliba

Dan wasan baya na Arsenal, William Saliba, ya bayyana cewa sha’awar da Real Madrid ta nuna masa na da matukar daukar hankali, amma burinsa shi...

Magoya bayan bangaren Wike sun mamaye hedkwatar PDP a Abuja

Wasu magoya bayan bangaren sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP, Mohammed Abdulrahman, sun mamaye hedkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja, a ranar Litinin suna rera...

Mafi Shahara