DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babu wani rikicin da ya dabaibaye PDP, kan ‘ya’yanta hade yake – Damagum

-

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum, ya yi watsi da ikirarin rikicin cikin gida a cikin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa jam’iyyar PDP ta ci gaba da kasancewa a dunkule duk da rahotannin da kafafen yada labarai ke yaɗawa kan rikicin jam’iyyar.

Damagum ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP a koda yaushe babbar jam’iyyar adawa ce, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta san yadda za ta magance duk wata matsalarta ta cikin gida idan ta ta so.

Google search engine

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da New Nigeria Peoples Party (NNPP) da suka koma PDP a kananan hukumomin Nguru da Bade a jihar Yobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sojojin Najeriya sun yi ajalin na hannun damar Bello Turji a Sokoto

Sojojin rundunar 8 Division na Najeriya sun tabbatar da shafe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, daga duniya, a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar...

Bai kamata Seyi Tinubu ya rika yawo da cincirindon sojoji ba – Wole Soyinka

Farfesa Wole Soyinka ya gargadi Shugaba Bola Tinubu da ya kula da yadda ake amfani da jami’an tsaro ga wasu mutane na musamman, musamman dangin...

Mafi Shahara