DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Babu wani rikicin da ya dabaibaye PDP, kan ‘ya’yanta hade yake – Damagum

-

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum, ya yi watsi da ikirarin rikicin cikin gida a cikin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa jam’iyyar PDP ta ci gaba da kasancewa a dunkule duk da rahotannin da kafafen yada labarai ke yaɗawa kan rikicin jam’iyyar.

Damagum ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP a koda yaushe babbar jam’iyyar adawa ce, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta san yadda za ta magance duk wata matsalarta ta cikin gida idan ta ta so.

Google search engine

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da New Nigeria Peoples Party (NNPP) da suka koma PDP a kananan hukumomin Nguru da Bade a jihar Yobe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Buhari mutum ne mai girmama al’adu da masarautu – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shiga sahun wadanda ke jimamin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a...

An rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat Buhari

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin girmamawa da...

Mafi Shahara