DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jiga-jigan APC sun tattaru a Abuja, sun tabbatar wa da Shugaba Tinubu zai yi nasara da gagarumin rinjaye a zaben 2027

-

Jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani gangami a Abuja, inda suka bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumin rinjaye a zaben 2027 mai zuwa.

Duk da cewa har yanzu Shugaba Tinubu bai kai rabin wa’adinsa na farko ba, kuma bai bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a hukumance ba, amma shugabannin jam’iyyar APC sun yi amfani da dandalin taron hadin kan babban birnin tarayya Abuja—wanda aka gudanar a filin wasa na Old Parade da ke Abuja, domin nuna goyon bayansu ga takararsa karo na biyu.

Google search engine

An shirya taron ne domin tarbar shugaban karamar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC) Hon. Christopher Zakka Maikalagu, kansiloli, da dubban magoya bayansu sun shigo jam’iyyar APC daga jam’iyyar adawa ta PDP.Da yake zantawa da manema labarai a wajen taron, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin maliya, ya bayyana kwarin gwiwar sake zaben Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Lakurawa sun yi ajalin makiyaya goma a jihar Kebbi

Aƙalla makiyaya goma ne aka ruwaito sun rasu a harin ramuwar gayya da aka kai wa Fulanin kauyen Tilli da ke Ƙaramar Hukumar Bunza ta...

PDP ta dage tantance ‘yan takara na babban taronta na kasa

Dagewar ta zo ne ’yan sa’o’i bayan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ayyana shirinsa na takarar shugabancin jam’iyyar, duk da cewa wasu...

Mafi Shahara