DCL Hausa Radio
Kaitsaye

PDP ta yanke shawarar goyon bayan Tinubu a 2027 domin ci gaban yankin mu da kasa baki daya- shugaban riko na jam’iyyar PDP a Bayelsa.

-

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa kuma Sakataren Yankin Kudu maso Kudu na jam’iyyar, George Turnah, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP a jihar za ta goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na shekarar 2027 — ko da kuwa Gwamna Douye Diri amince ba.

Turnah, wanda kuma shine jagoran kungiyar New Associates, wata kungiyar dake goyon bayan Nyesom Wike da aka kaddamar a jihar Bayelsa a karshen mako, ya ce mafi yawan gwamnonin Kudu maso Kudu suna marawa Shugaba Tinubu baya ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke ciki ba.

Google search engine

 

Yayin wani tattakin nuna goyon baya da suka gudanar a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, sakataren na PDP a wannan shiyya ya ce manufar taron shine godewa Shugaba Tinubu bisa yadda ya nada ‘ya ‘yan yankin Neja Delta a manyan mukaman gwamnati.

A cewar Turnah, lokaci yayi da Bayelsa za ta bayyana irin goyon bayan da take da shi domin tabbatar da ci gaba da wakilcin yankin Neja Delta a matakin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsare-tsaren Tinubu na farfaɗo da martabar Nijeriya a duniya -Kashim Shatima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na sake gina martabar Nijeriya a idon duniya tare...

Gwamnatin Nijeriya na shirin dakatar da shigo da kayan tsaro daga waje

Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa. Minista a ma'aikatar Tsaron...

Mafi Shahara