DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tinubu ya dauko hanyar kassara jam’iyyun adawa a Nijeriya – Sule Lamido

-

 

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma daya daga cikin wadanda aka kafa jam’iyyar PDP da su, Alhaji Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da amfani da karfin gwamnati wajen murkushe muryoyin ‘yan adawa, yana mai gargadin cewa hakan barazana ce ga dimokuradiyyar Najeriya.

Lamido ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Talata, inda ya ce cin zarafi da tsoratar da ‘yan adawa alamu ne na gwamnati raunin gwamnatin Tinubu wajen jurewa adawa.

Ya soki Shugaba Tinubu kan zargin amfani da dukiyar kasa wajen raunana jam’iyyun adawa, lamarin da ya bayyana a matsayin hatsari kuma abin da ya saba wa tsarin dimokuradiyya.

Dangane da yawan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki, Lamido ya ce ko a kwalarsu, yana mai cewa matsalar ta wuce bambancin jam’iyya.

Fadar shugaban kasa dai ta sha musanta wadannan zarge-zargen, tana mai cewa duk wanda ya fice daga jam’iyyar adawa ya yi hakan ne da kashin kansa ba tare da tilas ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dan Amurka na farko a tarihi Robert F. Prevost ya zama sabon Fafaroma

Robert Francis Prevost, dan asalin birnin Chicago a Amurka, an haife shi a ranar 14 ga Satumba, 1955, yana da shekaru 69 a yanzu. An nada...

Bill Gates zai rarraba kaso 99% na dukiyarsa ga jama’ar duniya

Attajirin nan na duniya Bill Gates, ya bayyana aniyarsa ta raba kaso 99% na dukiyar da ya mallaka da ta kai Dala bilyan 200, ga...

Mafi Shahara