DCL Hausa Radio
Kaitsaye

ACF ta gindaya sharadi ga ’yan takara masu neman goyon bayan Arewa a zaben 2027

-

Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana cewa yankin Arewa zai mara wa ɗan takara baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ne kawai idan ya nuna ƙwarin guiwar kare muradun yankin.

Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taro da kungiyar ta gudanar a Kaduna, inda aka tattauna kan manyan matsalolin da ke addabar Arewa da ma kasa baki ɗaya.

Google search engine

Alhaji Dalhatu, wanda kuma shi ne tsohon Ministan Lantarki da Karfe, ya jaddada cewa ACF ba za ta goyi bayan kowanne ɗan takara ko jam’iyya ba sai dai waɗanda suka nuna cikakken kishin yankin Arewa da niyyar magance matsalolinsa da suka hada da rashin tsaro, talauci da koma bayan tattalin arziki.

Ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta farka daga dogaro da alkawuran siyasa Mai kama da shificin gizo, tare da tabbatar da an zaɓi shugabanni masu gaskiya da rikon amana da za su kai yankin tudun mun tsira.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Babban Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yadda fitinar bayan zabe ta yi ajalin mutane sama da 700 a Tanzaniya

Jam’iyyar adawa ta Chadema a Tanzaniya ta bayyana cewa fiye da mutane 700 ne suka mutu cikin kwana uku na zanga-zangar bayan zaɓen shugaban ƙasa,...

Tinubu ya umurci sabbin hafsoshin tsaro da su murƙushe duk wata barazanar tsaro

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci sabbin hafsoshin tsaron da su tashi tsaye wajen murƙushe duk wata barazanar tsaro da ke tasowa a sassan...

Mafi Shahara