Bankunan kasuwanci a Najeriya sun ƙara kuɗin tura saƙon SMS zuwa Naira 6, daga Naira 4 da ake biya a baya.
Wannan ƙarin kuɗin na kunshe ne a cikin saƙonnin da wasu bankuna suka aikewa kwastomominsu a safiyar ranar Laraba, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Bankunan sun bayyana cewa ƙarin ya biyo bayan hauhawar farashin sadarwa da kamfanonin sadarwa suka sanar a baya-bayan nan.
Sai dai har yanzu CBN bai fitar da wata sanarwa kan matakin ba, yayin da kwastomomi ke bayyana damuwa kan yawan ƙarin kuɗin da suke fuskanta daga bankuna.