DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kada ka sake tsayawa takarar shugabancin Nijeriya – Shawarar Hakeem Baba Ahmed ga Atiku Abubakar

-

Tsohon mai ba shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da shugaban kasa mai ci, Bola Tinubu, da su janye daga aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027, tare da ba matasa masu kwarewa damar jagorantar kasa.

A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television, Baba-Ahmed ya bayyana cewa Atiku ya tsaya takarar shugaban kasa har sau shida ba tare da nasara ba, don haka ya kamata ya janye ya kuma tallafa wa matasa masu tasowa.

Google search engine

Haka kuma, Baba-Ahmed ya shawarci Tinubu da kada ya nemi wa’adi na biyu a 2027, yana mai cewa ya kamata ya Yi amfani da sauran lokacin mulkinsa wajen gyara kasa da kuma horar da matasa da za su gaje shi.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu is a highly skilled and experienced broadcast journalist and fact-checker. Ukashatu has over five years of experience in writing, editing, and presenting news and program content for radio and television. As a dedicated and hardworking professional, He is committed to upholding the values of accuracy, fairness, balance, independence, and accountability in her reporting and programs.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Buhari mutum ne mai girmama al’adu da masarautu – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shiga sahun wadanda ke jimamin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a...

An rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat Buhari

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin girmamawa da...

Mafi Shahara