DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An dage shari’ar zargin zamba kan tsohon minista Saleh Mamman saboda rashin tafinta-Daily Trust

-

An dage ci gaba da sauraron shari’ar Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, da ake yi a gaban kotun Tarayya da ke Abuja, sakamakon rashin mai fassara wato tafinta a kotun.

A lokacin da aka kira shari’ar a ranar Juma’a, Lauyan masu gabatar da kara, Barrister A.O. Mohammed, ya shaida wa kotu cewa duk da cewa an shirye ci gaba da sauraron shari’a, yana fuskantar cikas na rashin mai fassara.

Google search engine

Ya bayyana cewa an shaida masa cewa mai fassarar kotu na bakin aiki a wani muhimman taro na da aka tura shi.

Saboda haka, Lauyan ya roki kotu da ta bayar da ɗan gajeren lokaci don samun damar kawo mai fassara gabanin cigaba da shari’ar.

Lauyan da ke kare wanda ake tuhuma, Barrister Emmanuel Hassan, bai yi jayayya da bukatar ba.

A sakamakon haka, Mai shari’a James Omotosho ya dage sauraron karar zuwa ranakun 8 da 9 ga Mayu domin ci gaba da shari’a.

Hukumar EFCC ce dai ke tuhumar Saleh Mamman da laifuka 12 da suka shafi hada baki da karkatar da kudade ta ba bisa ka’ida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba...

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

Mafi Shahara