DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kada ku daka ta masu suka, ku yi aikin hidimtawa jama’arku kawai – Sakon Tinubu ga Gwamnonin Nijeriya

-

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnonin Najeriya da su mai da hankali kan ci gaban al’umma duk da sukar da ake musu, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki Jihar Katsina, inda ya kaddamar da titin Eastern Bypass mai nisan kilomita 24 da kuma Cibiyar Inganta Noma ta jihar da aka gina a karkashin Gwamna Dikko Radda.

Tinubu ya yaba da jajircewar Gwamna Radda a fannonin noma, lafiya, ilimi da gine-gine, duk da barazanar tsaro da jihar ke fuskantar, inda ya ce gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan kokarin jihar wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.

Google search engine

Shugaban ya bayyana cewa yunwa da talauci na ci gaba da zama barazana ga zaman lafiya, kuma gwamnatin sa na aiki tukuru wajen tabbatar da wadatar abinci ta hanyar bunkasa noman zamani da inganta tsarin ruwa.

A karshe, Tinubu ya sanar da cewa ana farfado da Bankin Noma domin bai wa manoma rance cikin sauki. Ya kuma bukaci sauran gwamnonin Najeriya su dauki darasi daga tsarin da Katsina take bi wajen yaki da talauci da yunwa a kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara