DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An fadi dalilin da ya sa dan sandan da ke yi wa Ganduje dogari ya sunkuya ya daura masa takalma a kafa

-

Mataimaki na Musamman ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, kan harkokin sadarwa Aminu Dahiru Ahmad, ya kare dan sanda da aka gani yana daura wa shugaban jam’iyya takalmi.

Bidiyon da ya nuna dan sandan a duke gaban Ganduje yana daura masa takalmi ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Google search engine

Aminu Dahiru Ahmad ya ce shaidun gani da ido sun tabbatar cewa dan sandan ya kai dauki ga takalman Ganduje ne domin tabbatar da tsaron lafiyarsa.

Ya ce sabanin abin da wasu ke yayatawa, Ganduje yana girmama masu taimaka masa da ma’aikatan gidansa matuka.

Aminu Dahiru ya ce, wannan gajeren bidiyo dai shaida ce da ke nuna yadda kyakkyawar alaka take tsakanin Dr Abdullahi Umar Ganduje da masu taimaka masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara