An gurfanar da wata mata a gaban Kotun shari’ar musulunci da ke Post Office a cikin birnin Kano bisa zargin auren maza biyu a lokaci guda.
Harira Muhammad Tudun Murtala da mijinta na farko, Sagiru Shuaibu Tudun Murtala, sun yi aure na tsawon watanni shida suna kuma zaune kowa da gidansa kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Lokacin da mijin nata na farko ya ziyarce ta ne ya tarar da wani namiji a dakin matarsa, inda ya sanar da makwabta abin da ke faruwa.
Lokacin da ta bayyana a gaban kotu, matar da farko ta musanta cewa tana aure da mijinta na farko, amma da alkalin kotun ya umurci ta rantse da Alkur’ani, sai ta daina jan maganar.
Mijin na biyu, Bello Abdullahi Yankaba, ya shaida wa kotu cewa kawunta, wani Abdullahi Umar, ne ya daura aure tsakaninsu bayan ya biya sadaki na Naira dubu dari.
Alkalin kotun, Khadi Munzali Tanko Soron Dinki, ya bayar da umurnin ci gaba da bincike daga ‘yan sanda tare da ba da umurni a ci gaba da tsare matar da mijinta na biyu har zuwa ranar 16 ga Mayu a gidan gyaran hali.