DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Akalla yara miliyan ɗaya ne, a jihohin Borno, Adamawa da Yobe ke fuskantar barazanar kamuwa da matsananciyar yunwa- Gwamnatin Nijeriya

-

Akalla yara miliyan ɗaya a jihohin Borno, Adamawa da Yobe (BAY) na cikin barazanar kamuwa da matsananciyar yunwa (severe acute malnutrition – SAM) a shekarar 2025, adadi wanda ya ninka wanda aka samu a shekarar da ta gabata, 2024.

Cikin wannan adadin, sama da yara 600,000 na fuskantar barazana cikin watanni shida masu zuwa, inda rahoton yayi gargadin cewa muddin ba’a samu tallafin gaggawa ba, akwai yuwuwar mutuwar da dama ciki.

Google search engine

Binciken Cadre Harmonisé da Gwamnatin Najeriya ta jagoranta kuma aka fitar da sakamakonsa a watan Maris 2025, ya nuna cewa mutane miliyan 4.6 a jihohin Borno, Adamawa da Yobe za su fuskanci matsanancin ƙarancin abinci tun daga watan Yuni, lokacin da ake kira lokacin fatara.

A baya bayan nan, ministan harkokin jinƙai da rage talauci, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, tare da wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Malick Fall, sun ƙaddamar da shirin daukin gaggawa a Abuja, wanda zai buƙaci dala miliyan 159 (fiye da naira biliyan 230) don tallafa wa mutane miliyan biyu da ke cikin tsananin buƙata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050,...

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba...

Mafi Shahara