DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Yaron shago ya yi wa ‘yan mata 10 ciki, daga cikinsu hada diyar ogansa a Anambra

-

Wani matashi ɗan shekara 18, da aka tura don koyon sana’a a jihar Anambra, ya shiga hannun hukuma bayan zargin dirkawa mata 10 ciki a watanni biyar kacal, wanda ya haɗa da ‘yar ubangidansa da abokiyar zamansa a shagon sana’ar.

Kwamishinar Mata da Jin Daɗin Jama’a ta jihar Anambra, Ify Obinabo, ta bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ta watsa kai tsaye a kafar sada zumunta a ranar Laraba, lamarin ya faro ne tun bayan da aka tura matashin zuwa koyon sana’a.

Google search engine

Bayan wata uku kacal da fara koyon sana’ar, matashin ya ke bibiyar ‘yar maigidansa da kuma wata zaman shago, lamarin da ya sa aka kori shi daga wurin koyon sana’ar.

Bayan ya koma gari, Kwamishina Obinabo ta ce lamarin ya kara ta’azzara, inda tace uwar yaron ce ta zo ofishinta don neman mafita.

Obinabo ta bayyana cewa bata iya magance lamarin ita kadai ba, ta kuma nemi shawarwari daga jama’a don gano mafita – tana tambayar ko akwai wani al’amari na ruhanai da ke tattare da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun yi nadamar yekuwar a ba Yilwatda shugabancin APC – Kungiyar magoya bayan jam’iyyar na Arewa ta tsakiya

Kungiyar magoya bayan jam'iyyar APC a Yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta bayyana nadamarta bayan ta dage kai da fata sai an naɗa dan yankin...

Kungiyar tarayyar Turai za ta tallafa ma gwamnatin Nijeriya da Yuro miliyan 45 don inganta fasahar zamani

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) tare da abokan huldarta sun kaddamar da sabon mataki na hanzarta sauyin fasahar dijital a Nijeriya, yayin taron kwamitin kula da...

Mafi Shahara