DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar SON ta kama tayoyi da wayoyin lantarki na jabu a Nijeriya

-

Hukumar SON mai kula da ingancin kaya a Nijeriya ta ja hankalin cewa akwai tayoyi da wayoyin lantarki marasa inganci da ke yawo cikin kasar.

Babban daraktan hukumar Dr Ifeanyi Chukwunonso Okeke ne ya bayyana damuwarsa da wannan lamari a lokacin da ya jagoranci lalata wasu tayoyi da wayoyin lantarki da wasu kayayyaki marasa inganci da kimarsu ta kai ta bilyoyin Naira a jihar Legas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Google search engine

Ya koka kan yadda ake samun karuwar kaya marasa inganci da kuma na jabu a manyan kasuwannin da ke fadin kasar, tare da zargin wasu da ya kira masu zagon kasa ga tattalin arzikin kasa da daukar alhakin shigo da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ministan yada labarai ya nesanta kansa da wani rubutu mai taken “Malagi 2027”

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya, Mohammed Idris, ya nesanta kansa daga wani rubutu na siyasa mai taken “Malagi 2027”, wanda...

Wasu tsoffin ‘yan sanda sun roki Tinubu da ya sa a mayar da su aiki bayan tilasta yi musu ritaya

Wasu tsoffin jami’an rundunar ’yan sandan Nijeriya sun sake kira ga rundunar da ta bi hukuncin Kotun Kwadago ta Kasa, wadda ta bayar da umarnin...

Mafi Shahara