‘Yan majalisar wakila uku daga jihar Katsina sun bar jam’iyyarsu ta PDP sun koma APC.
‘Yan majalisar su ne Ali Iliyasu na Safana/Batsari/Danmusa, Salisu Yusuf Majigiri na Mashi/Dutsi da Abdullahi Balarabe na Bakori/Danja.
Kakakin majalisar wakilan Tajuddeen Abbas ne ya karanta sanarwar ficewar ta su.
‘Yan majalisar dai sun bayyana rikicin da ya addabi jam’iyyar PDP ne ya sa suka bar ta. Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya ziyarci majalisar don gane wa idonsa yadda ‘yan majalisar suka sauya sheka suka koma jam’iyya mai mulki.