Zafin kishi ya sa wani magidanci ya kashe tsohuwar matarsa kuma ya kashe kansa bayan an daura mata aure da wani mijin na daban a kauyen Barago da ke cikin karamar hukumar Mirriah ta jihar Damagaram a Jamhuriyar Nijar.
Lamarin ya auku ne a ranar Larabar makon nan 7 ga watan Mayu nan da misalin karfe 10 zuwa 11 na safe.
Rahotanni DCL Hausa ta samu daga wadansu mazauna garin sun ce matar tana da ‘ya’ya wajen bakwai da tsohon mijin nata da ya yi ajalin ta a ranar da aka daura mata auren da wani sabon angon nata.