Hukumar dake lura da birnin tarayya Abuja FCTA ta ce ofisoshin jakadanci 34 ne a Abuja ke fuskantar rufewa saboda kin biyan harajin fili sama da shekara 10.
Rahoton DW Afirka ya ce kafin yanzu ministan Abuja Nyesom Wike ya umurci a dauki mataki kan gine-gine 4,800 da suka ki biyan haraji, duk da sassaucin kwanaki 14 da Shugaba Tinubu ya bayar, wanda yanzu ya kare.
Kasashen da suka fi ki biyan haraji sun hada da Ghana, Thailand, Rasha, Turkiyya, Jamus, India, China, Saudiyya, Egypt, Habasha, Sudan, Nijar, Kenya, Zimbabwe, da Afrika ta Kudu inda wssu daga cikinsu suka musanta zargin.