Jam’iyyar NNPP a Nijeriya ta bayyana cewa dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ba ya da damar amfani da ita don yin takarar shugaban kasa a shekarar 2027.
Tsagin jam’iyyar na bangaren Dr Agbo Major, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito cewa Dr Major na mayar da martani ne kan ikirarin da Buba Galadima ya yi cewa Kwankwaso zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar NNPP tare da yin takarar shugaban kasa karkashinta a zabuka na gaba.