Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiDakarun sojin Nijeriya sun yi ajalin 'yan bindiga 3, tare da kwato...

Dakarun sojin Nijeriya sun yi ajalin ‘yan bindiga 3, tare da kwato makamai a Filato

Sojojin Operation Safe Haven (OPSH) sun kawar da wasu ‘yan bindiga guda uku a kauyukan Teng da Kayarda na karamar hukumar Qua’an Pan, a jihar Filato.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Samson Zhakom, ya bayyana cewa an kai harin ne da safiyar Talata bayan samun sahihan bayanan sirri kan shirin ‘yan bindigar na kai farmaki.

An kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu, magazine hudu da harsashi 56 daga hannunsu.

Zhakom ya ce rundunar na ci gaba da neman sauran ‘yan kungiyar da suka tsere kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tabbatar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata