Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiZan dauki tsauraran matakai, in ji sabon shugaban APC

Zan dauki tsauraran matakai, in ji sabon shugaban APC

Sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa zai dauki wasu muhimman matakai masu tsari domin sake gina jam’iyyar da tabbatar da shugabanci nagari.

Da yake zantawa a shirin Politics Today na Channels TV, Yilwatda ya ce sabon jagorancinsa zai kasance mai gaskiya da tsauri, tare da bude kofa ga kowa, ciki har da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da duk wanda ke da sha’awar sauya sheka zuwa APC.

Farfesa Yilwatda ya kuma bayyana cewa a halin yanzu babu wata jam’iyya mai karfin da za ta iya karawa ko kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, yana mai cewa APC na da cikakken tsari da goyon bayan jama’a don ci gaba da mulki.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata