Tuesday, April 7, 2026
HomeLabarai'Yan bindiga sun kai hari kayuka 16, sun yi ajalin mutum 5,...

‘Yan bindiga sun kai hari kayuka 16, sun yi ajalin mutum 5, sun yi garkuwa da wasu da dama a jihar Zamfara

‘Yan bindigar da suka kai hari a akalla garuruwa 16 tsakanin Asabar da Lahadi, a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara sun yi aja mutane 5 tare da yin garkuwa da mata da dama.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa a ranar Asabar, ‘yan bindigar sun farmaki garuruwa 8 ciki har da Dan Isa, Kyatawa, Tudu, Gidan Haruna, da sauransu, inda suka kashe mutum 1 a Gidan Haruna kuma suka sace mata 8.

A ranar Lahadi kuma, sun sake dawowa Kwalau inda suka kashe mutum 4 — Abubakar, Murtala, Aminu da Bello — tare da raunata wani Ashafa, wanda aka kai asibitin Kaura Namoda.

Rahotan jaridar Daily Trust ya ce ‘yan sa-kai sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar a daren Asabar, lamarin da ya sa suka ja da baya.

Sai dai, da safe sun dawo cikin shiri, inda suka kai farmaki wajen taron ‘yan sa-kai, inda suka kashe 4, suka raunata 1, tare da sace mata da kwashe kayan abinci da na gida.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata