Monday, April 6, 2026
HomeKetareFilin jirgin saman Mexico ya dakatar da aiki sakamakon ambaliyar ruwa

Filin jirgin saman Mexico ya dakatar da aiki sakamakon ambaliyar ruwa

Filin jirgin saman kasa da kasa na Benito Juarez na birnin Mexico ya dakatar da aiki na sa’o’i da dama a Litinin din nan, bayan da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye babban birnin kasar tare da haifar da rashin kyan yanayin kamar yadda hukumomin suka shaida.

Sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a yammacin Lahadi, bisa rahotannin hukumar kula da zirga-zirgar Jiragen sama ta ba da umarnin dakatar da sauka da tashin Jiragen sama na tsawon sa’o’i 3 masu zuwa, an bayyana haka ne a shafin X na jami’in tashar jirgin kafin karfe 9:00 na dare agogon GMT.

Filin jirgin saman kasa da kasa na Benito Juarez, daya daga cikin filayen jiragen sama na kasa da kasa guda biyu na birnin, kuma daya ne daga cikin mafi tara mutane wurin zirga-zirgar Jiragen sama a kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata