Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwaji ya nuna cewa wani direban jirgi da ke aiki da Air...

Gwaji ya nuna cewa wani direban jirgi da ke aiki da Air Peace na tu’ammali da kwayoyi

Hukumar bincike ta sufurin jiragen sama ta Nijeriya NSIB ta fitar da rahoto kan saukar gaggawa da jirgin Air Peace ya yi a filin jirgin sama na Port Harcourt, inda ta gano cewa matukin jirgin da mataimakinsa sun sha giya da kuma amfani da kwayoyi kafin tashin jirgin.

Rahoton ya ce ranar 13 ga Yulin 2025, jirgin Air Peace ya taso daga Legas zuwa Port Harcourt dauke da fasinjoji 103.

Lokacin da jirgin ya iso filin jirgin saman Port Harcourt, matukan sun kasa daidaita saukar jirgin, lamarin da yasa jirgin ya sauka ba daidai ba maimakon yadda jirgi ya saba sauka.

Lamarin ya tayar da hankali a tsakanin jama’a da masana harkar sufurin jiragen sama, inda ake ganin ya kamata hukumomi su tsaurara dokoki kan gwajin matuka kafin su hau jirgi.

Wasu kwararru sun bayyana cewa shan giya ko kwayoyi na kawo jinkiri ga tunani, daidaito da kuma saurin daukar mataki, wanda dukkaninsu muhimmai ne ga aikin matukan jirgi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata