’Yan bindiga sun sake farmakar wani kauye a jihar Kano, inda suka yi garkuwa da mutane 11 a Unguwar Tsamiya (Dabawa), da ke ƙaramar hukumar Shanono.
Rahotanni daga mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na daren Litinin, inda maharan suka dinga harbe-harbe ta sama tare da dukan wasu daga cikin mutane kafin su yi awon gaba da mutum 11, maza tara da mata biyu sannan suka yi awon gaba da shanu biyu.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa lamarin ya faru ne kwanaki kalilan bayan wani farmakin da aka kai ‘Yan Kamaye a ƙaramar hukumar Tsanyawa, wani yanki da ke iyaka da jihar Katsina.



