‘Yan kwangila sun girke akwatin gawa a kofar shiga ofishin ma’aikatar kudin Nijeriya da ke Abuja.
‘Yan kwangilar, karkashin inuwar kungiyarsu ta ‘yan asalin Nijeriya sun fara zanga-zangar lumana a ma’aikatar a ranar Talata, suna neman gwamnatin tarayya ta biya su bashin da suke bin ta.
Daily Trust ta ruwaito cewa sun bayyana akwatin gawar da suka ajiye a matsayin wata alama da ke nuni da yadda mambobinsu ke rasa rayukansu sakamakon halin kuncin da suke ciki.
