Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya na sa ran tara Naira tiriliyan 34 daga kudaden shiga...

Gwamnatin Nijeriya na sa ran tara Naira tiriliyan 34 daga kudaden shiga a 2026

Majalisar zartaswa ta Nijeriya ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar na sa ran tara Naira tiriliyan 34.33 a shekarar 2026.

Ministan tsare-tsaren kasafi, Atiku Bagudu be ya sanar da hakan bayan zaman majalisar da shugaba Tinubu ya jagoranta, inda ya ce ofishin kasafin kasa ne ya gabatar da takardun ta hannun Darakta-Janar, Tanimu Yakubu.

Bagudu ya ce majalisar ta ɗauki matsayar samar da ganga miliyan 2.06 na mai a rana a 2026, sai dai don kauce wa gibin kudaden shiga, za a yi amfani da adadin ganga miliyan 1.8 wajen tsara kasafi.

Majalisar ta kuma amince da farashin gangar mai na Dala 64 da kuma musayar Naira 1,512 kan Dala ɗaya, la’akari da tasirin zaben 2027 kan darajar Naira.

Ministan ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya na sa ran tara kuɗaɗen shiga daga fannonin da ba na mai ba, inganta haraji, da faɗaɗa tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata