Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiSufeta Janar na 'yan sandan Nijeriya ya bada umurnin bincike kan zargin...

Sufeta Janar na ‘yan sandan Nijeriya ya bada umurnin bincike kan zargin cin zarafi da hallaka masu zanga-zanga da Amnesty International ta yi

 

Sufeta Janar na ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ya bayarda umurnin yin bincike kan zarge-zargen cin zarafi da kisa da kuma kama masu zanga-zangar matsin rayuwa da ta faru a fadin kasar.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a cikin wani rahoto da ta fitar a kwanannan, ta zargi rundunar ‘yan sanda da amfani da karfin da ya wuce iyaka a yayin zanga-zangar matsin rayuwa da ta faru daga 1 zuwa 10 ga watan Augustan 2024, da yayi sanadiyar mutuwar mutum 24 a jihohin Borno, Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa da kuma Niger.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ACP Olumiyiwa Adejobi ya fitar a Abuja, ya ce akwai alamun shakku da kuma karya a zargin da Amnesty International ta yi, inda ya ce Kayode Egbetokun ya bada umurnin yin bincike domin gano gaskiyar lamari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata