Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta cafke wani likita da ake zargi da bai wa masu garkuwa da mutane wadanda suka ji rauni kulawa a cikin daji.
Likitan da ake zargi wanda ba a bayyana sunansa ba, an cafke shi ne a yankin Jebba bayan bayanan sirri sun nuna cewa wasu masu aika saƙo suna kai kayan magani daga Sokoto domin jinya ga ‘yan ta’adda da suka ji rauni a dazuzzuka cikin jihar Kwara.
Majiyoyin tsaro sun ce da yawa daga cikin waɗannan kungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga ne a yayin arangama da jami’an tsaro a kwanan nan.
Daily Trust ta ruwaito cewa da yake tabbatar da faruwar lamarin, Mai magana da yawun gwamnan Jihar Kwara, Rafiu Ajakaye, ya ce kama wanda ake zargin wani gagarumin ci gaba ne a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na yaƙi da ta’addanci.
