Hukumar JAMB ta fitar da cikakkun ka’idoji da matakan rajistar Jarrabawar UTME ta 2026, tare da jerin matsalolin da ɗalibai kan fuskanta wajen rajista.
Sanarwar ta fito ne ta shafinta na X a ranar Lahadi domin taimaka wa masu niyyar shiga jarrabawar su shirya tun da wuri.
JAMB ta ja kunnen ɗalibai su tabbatar da cewa duk bayanansu sun dace NIN, imel, da sakamakon A-Level, kafin su tura NIN don samun profile code.
Da zarar an samu profile code, ba za a iya canza shi ba, kuma bayanan ɗalibi za su fito kai tsaye daga NIMC.
Daga nan ɗalibai su je ofishin JAMB mafi kusa ko CBT Centre da aka amince da shi domin kammala rajista.
Ana sa ran fara siyar da fom ɗin UTME na 2026 daga Jumma’a, 31 ga Janairu, 2026, zuwa Asabar, 8 ga Maris, 2026.
