DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ciwon suga ya yi sanadin rasa rayukan sama da mutane 55,000 wannan shekarar a Nijeriya

-

Google search engine
Kwararre kan ciwon suga da ake kira Diabetes a turance, Farfesa Olufemi Fasanmade na asibitin koyarwa ta jami’ar jihar Lagos ya ce sama da mutane 55, 000 ne su ka mutu sanadiyar cutar a wannan shekara.
Ya bayyana hakan ne a yayin da ‘yan jarida ta yanar gizo kan cutar ‘diabetes’ suke yi masa tambayoyi, wanda kamfanin magani na Novo Nordisk ya shirya.
Farfesa Fasanmade ya ce a shekara ta 2021 mutane 48,375 suka mutu, a shekara ta 2022 kusan mutane 50,000 suka mutu yayinda a shekara ta 2023 kusan mutane 53,000 su ka mutu sanadiyar cutar suga.
A cewar kwararren daga cikin mutum miliyan 24 da ke fama da cutar a Afrika, mutum miliyan 4 daga Nijeriya suka fito kuma ana hasashen cewa yawan su zai karu nan da shekaru 20.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Paul Biya ya yi wa masu zanga-zangar sakamakon zabe shagube a Kamaru

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, ya yi shagube ga rikicin siyasar da ke faruwa bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe sakamakon zaɓen shugaban...

Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sallami mai horaswarta Igor Tudor

Kungiyar Juventus ta sallami kocinta Igor Tudor a ranar Litinin bayan shan kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, wanda ya sa kungiyar ta tara...

Mafi Shahara