DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiHukumar EFCC za ta sake gurfanar da Yahaya Bello kan badakalar biliyan...

Hukumar EFCC za ta sake gurfanar da Yahaya Bello kan badakalar biliyan N80.02

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC za ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja a yau.
Za a gurfanar da Yahaya Bello ne tare da wani makusancinsa da wasu mutum biyu Dauda Suleiman da kuma Abdulsalam Hudu, a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite a kan zarge-zarge 19 na badakalar kudi naira biliyan 80.0.
Ko jiya Alhamis, sai da hukumar ta gurfanar da Yahaya Bello ne tare da wasu mutane biyu akan zarge-zarge 16 wadanda suka musanta aikatawa.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata