Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati a Nijeriya EFCC za ta gurfanar da tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, a kotun babban birnin tarayya da ke Gwarinpa, kan zargin almundahana da cin hancin da ya kai N2.26bn.
Ngige na fuskantar tuhume-tuhume guda takwas, ciki har da amfani da mukami wajen fifita kamfanonin abokansa yayin da yake kula da NSITF daga 2015 zuwa 2023.
EFCC ta ce ya ba wa kamfanonin Cezimo Nigeria Ltd, Zitacom Nigeria Ltd, Jeff & Xris Ltd, da Olde English Ltd kwangiloli na biliyoyin Naira ba bisa ka’ida ba.
Rahoton na jaridar Punch haka nan ya ce ana zarginsa da karɓar gudummawar kuɗi daga wasu kamfanonin kwangila a 2022, ciki har da N38.6m, N55m da N26.1m ta hanyar wasu shirye-shiryensa.
Kazalika an ruwaito cewa ana sa ran Ngige zai gurfana a kotu domin karanto masa kunshin tuhumar da ke kansa.
