Neman tazarce a 2027, ne ke hana ni korar jami’an da ba su da amfani a gwamnatina – In ji Gwamna Umar Bago
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sake jaddada goyon bayansa ga tsarin wa’adin zangon mulki guda ɗaya ga gwamnoni a Nijeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi na cewa wannan mataki zai ƙara inganta ayyuka, ya ƙara himma, kuma ya kawo ƙarshen rikice-rikicen neman tazarcen mulki da ke rage wa gwamnati aiki yadda ya kamata.
