Mazauna Jihar Sokoto sun koka kan tashin kudin haya, suna cewa lamarin na jinkirta aure tare da jefa matasa cikin matsin tattalin arziki da barazanar tarbiyya. Sun ce a al’adar jihar, yawancin samari ba sa aure sai sun samu gida, amma tsadar filaye da kayan gini ya sa hakan ya gagara.
‘Yan kasuwar gidaje sun ce ko mafi karancin haya ya wuce karfin talakawa, inda daki daya ke kaiwa ₦300,000, self-contain ₦400,000, yayin da gidaje masu dakuna biyu ke kaiwa ₦1.5–2m a shekara.
Dalilin haka ne wasu gidaje ma ke zaune babu masu haya saboda tsadar da ake sanya musu a cewar Rahoton Daily Trust.
Shugaban Hisbah na jihar ya ce suna tattaunawa da masu ruwa da tsaki don a sassauta tare da samar da gidaje masu saukin kudi da kuma daidaita kudin haya.
Gwamnatin Sokoto ta ce tana gina gidaje 1,000 da kuma kammala wasu 500, yayin da gwamnatin tarayya ke gina gidaje 250, amma mazauna na bukatar a tabbatar da adalci da gaskiya wajen rabon su.
