DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Za a dakatar da daliban da ke tsangwamar abokan karatunsu – Gwamnatin Nijeriya

-

Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta yi gargadin cewa duk dalibin da aka samu da laifin cin zarafin da ya kai ga taba lafiyar abokan karatunsu, za a dakatar da shi daga kwalejojin tarayya har sai yadda hali yayi.
Wata takardar umurni da babban sakataren ma’aikatar, Nasir Gwarzo, ya sanyawa hannu ta ce ba za su zuba ido dalibai na raunata junansu ba a cikin makarantu.
Sanarwar ta ce ko a ranar 7 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta bada umurnin dakatar da wasu dalibai 13 na tsawon makonni 6 a jihar Enugu har sai an gudanar da bincike kan zargin da ake musu na tsangwamar abokan karatunsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ba gasa muke yi da kamfanin NNPCL ba – Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa matatar man fetur dinsa ba ta yin gasa da Kamfanin man Fetur na Nijeriya, wato...

Hukumomin mulkin sojan Nijar sun kama wasu ‘yan jarida uku na Radio Sahara da ke jihar Agadez

Rahotanni daga gidan Radio Sahara Fm da ke jihar Agadez sun tabbatar da kama wasu 'yan jaridar gidan radiyon guda uku da suka hada da...

Mafi Shahara