DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kungiyar “Independent Hajj Reporters” ta bukaci NAHCON ta kafa kwamitin da zai sanya ido kan yadda za’a mayarwa mahajjata kudadensu

-

Kungiyar nan mai sanya ido kan harkokin aikin hajji a Nijeriya “Independent Hajj Reporters” ta yi kira ga hukumar alhazzai ta kasa NAHCON da ta kafa wani kwamiti na musamman da zai san ya ido akan aikin mayarwa mahajjata 95,000 da suka yi aikin hajji a shekara ta 2023 kudaden su.
 
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Ibrahim Muhammad, ya ce wannan ya zama tilas domin magance duk wasu korafe-korafe da ke biyowa bayan an mayar da kudade.
  
A saboda haka shugaban kungiyar Ibrahim Muhammad ya bukaci NAHCON ta fitar da bayanan kudin da ta tura, kuma ta tilastawa hukumomin bayyana yawan mutanen da za a mayarwa kudaden tare da kafa wani kwamiti da zai kunshi har da ‘yan jarida da zai tabbatar da cewa an biya mahajjatan hakkokinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

El-Rufai ya nemi Ribadu ya yi karin haske kan ‘gubar’ thallium sulphate mai matukar hatsari

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da ya fayyace rahotannin...

Hadin kan siyasa na karuwa a Kano – Gwaman Kano

Gwamnan Kano State, Abba Kabir Yusuf, ya ce ana samun ci gaba a hadin kan siyasa a jihar, yana mai fatan rikicin masarautar Kano zai...

Mafi Shahara