DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedMasu dauke da cutar HIV miliyan 1.6 ne daga cikin mutum miliyan...

Masu dauke da cutar HIV miliyan 1.6 ne daga cikin mutum miliyan 2 ne ke karbar magani a Nijeriya

Shugaban hukumar da ke yaki da cuta mai karya garkuwa jiki a Nijeriya Dr Temitope Ilori, ta ce akalla mutum miliyan 1.6 ne daga cikin mutane miliyan biyu dake fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV, ke karbar magani a Nijeriya.
Dr Temitope Ilori, ta ce wannan cutar ta fi kama wadanda ke tsakanin shekaru 15 zuwa 65, kuma karfin yaduwarta a kasar yana kashi 1.4
Ta bayyana hakan ne a wurin wani taro da aka shirya gabanin bukin ranar yaki da cutar AIDS da ya gudana a Abuja.
An ware ranar 1 ga watan Disamban kowace shekara ne domin wayar da kan al’ummar duniya akan irin hadarin wannan cutar tare da karfafawa wadanda ke rayuwa da wannan cutar mai karya garkuwar jiki.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata