DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya rubuta wa majalisa, yana neman ta amince da nadin Janar Oluyede a matsayin babban hafsan sojin kasa na Nijeriya

-

A cikin wasikar da ya rubuta wa shugaban majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Hon Tajuddeen Abbas, Shugaba Tinubu ya bukaci majalisun sun tabbatar da nadin bisa la’akari da tanadin doka a sashe na 218(2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da aka yi wa gyara a 1999 da kuma sashe na 18(1) na dokar da ta kafa rundunar soji.
Shugaba Tinubu dai ya nada Janar Oluyede a matsayin mukaddashin babban hafsan sojin kasa na Nijeriya a ranar 30 ga watan Oktoba, 2024 bayan jinya da Janar Lagbaja ya tafi, ba a ma jima ba, Janar Lagbaja ya rasu a ranar 5 ga watan Nuwamba.
Kafin nadin nasa, Janar Oluyede shi ne kwamandan rundunar sojin kundumbala da ke Jani, jihar Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050,...

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba...

Mafi Shahara