Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta yi watsi da kalaman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, inda ya ce jam’iyyarsa za ta sanya ido kan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) gabanin zaɓen 2027.
Da yake magana da jaridar PUNCH a ranar Lahadi, kakakin APC a Kano, Ahmad Aruwa, ya bayyana kalaman Kwankwaso a matsayin “marasa ma’ana kuma ba dole ba,” yana mai cewa tsohon gwamnan ya riga ya rasa tasiri a harkokin siyasar Nijeriya. Aruwa ya ce Kwankwaso ba shi ne halastaccen jagoran NNPP ba, kuma ba ɗan takarar kowace jam’iyya ba ne a halin yanzu.
A cewarsa, APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun riga sun kammala dukkan shirye-shiryen da za su tabbatar da nasara a Kano, yana mai cewa jam’iyyar na da cikakken ƙwarin gwiwa ga INEC.
Aruwa ya zargi Kwankwaso da ƙoƙarin raunana amincewar jama’a ga tsarin zaɓe, tare da kira ga al’umma da su yi watsi da kalamansa.
